Shugaban riko na Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC, Ibrahim Magu ya ce babu wasu shafaffu da mai a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa.
Ya ce, Abdulrashid Maina, tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa kan kudaden fansho, tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal da kuma Ayo Oke tsohon shugaban hukumar leken asiri ta Najeriya har yanzu suna fuskantar bincike
