Majiyar NAIJ.com ta ruwaito yan fashin sun dira bankin ne da misalin karfe 3 na rana, inda suka bude wuta suna harbin iska, suka tartwasa kofar bankin da nakiya, wanda ya shafi wata mota dake ajiye a kusa da kofar
Daga nan ne fay an fashin suka kutsa kai cikin bankin, inda suka tattara makudan kudade suka yi awon gaba da su. Haka zalika, baya da mutanen da suka kashe, yan fashin sun sanadiyyar samun raunin mutane da dayawa, inda suka kashe sama da awa guda suna tafka ta’asarsu inda mutane 2 suka rasa rayukansu
