shugabannin addinin krista sun nuna damuwarsu game da yanayin da kasar kamaru ke ciki musamman ma yankunan sashin inglishi inda yau sama da shekara guda kenan da rikici ya barke a wannan sashin renon inglishi da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tsakanin jami'an tsaro da yan aware da ke neman samun yancin yankunan biyu
shugabannin addinin sun bukaci zaman sulhu na gaggawa domin shawo kan lamarin da ya jima yana addabar al'ummar yankunan arewa maso yamma da kudu maso yamma inda mutane sama da dubu 15 suka daga muhallinsu na shiga makwabciyar kasar najeriya domin samun mafaka mai inganci
