Ministocin kudi da masana dabarun tsara manufofi na kasashen Afrika sun kammala taron karawa juna sani na kwanaki 5 a Addis Ababa na kasar Habasha, inda suka jaddada aniyarsu na amfani da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci wato AfCFTA a takaice.
Taron da ke da taken "yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci na kasashen Afrika don samar da guraben ayyukan yi da fadada hanyoyin tattalin arziki", ya tabo batutuwa masu yawa da suka hada da batun aikin gona, samar da kayayyakin more rayuwa, yaki da zambar kudade, da samar da dabarun bunkasa cigaban yankin Sahel.
Domin jaddada muhimmancin rawar da hukumomi masu zaman kansu za su bayar wajen cimma nasarar yarjejeniyar ta AfCFTA, hukumar kula da raya tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), ta bukaci a dauki kwararan matakai cikin hadin gwiwa don habaka cigaban harkokin cinikayya a nahiyar.
