Jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai shiga tsakani a yankin Zirin Gaza ya jaddada cewa: Al'ummar Palasdinu suna cikin halin kunci a yankin Zirin Gaza
A jawabinsa a gaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya kan halin da yankin gabas ta tsakiya ke ciki: Nikolay Mladenov ya bukaci gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da ta kawo karshen matakan wuce gona da irin da take dauka kan al'ummar Palasdinu musamman a yankin Zirin Gaza.
Mladenov kuma tofin Allah tsine kan ci gaba da kashe kananan yara da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a yankin musamman a lokacin gudanar da zanga-zangar lumana.

Tun daga ranar 30 ga watan Maris zuwa yanzu Palasdinawa fiye da 112 ne suka yi shahada, yayin da wasu kimanin 13,000 suka jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Gaza.