Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce hakika tsohon Gwamna Sanata Rabi’u Kwankwaso ya taimake shi a shekarun da suka shafe suna siyasa tare.
Ganduje ya shaida wa BBC cewa sun shafe fiye da shekara 20 suna tafiyar siyasa tare da tsohon mai gidan nasa.
“Mun shafe shekaru muna siyasa tare… kuma ya taimake ni, ni ma na taimake shi, a zaman da muka yi,” in ji Ganduje.
