An dade ana rade-radin cewar shugaban mai shekaru 73 zai tsaya takarar, amma ya ki cewa komai har sai a daren jiya da ya shaida wa al’ummar kasar ta kafar talabijin aniyarsa.
Mutane sama da 12 suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar, cikin su har da shugaban 'yan adawa Soumaila Cisse, wanda tsohon ministan kudi ne da Modibbo Kone, jami’in bankin Afrika ta Yamma.

Tun shekarar 2013 ake saran gudanar da zabe amma ake dagewa saboda matsalar tsaron da ta addabi kasar.