Yau ladahi 20 ga watan mayu 2018 Karo na 46 Kenan da kasar kamaru ke gudanar da bikin hadin kan kasa.
Shugaban kasar Paul Biya, Wanda ya kwashe shekaru 35 yana kan karagar mulki ne ya jagoranci bikin a babban birnin kasar Yaoundé.

Wannan bikin bana, ya zo daidai da lokacin da kasar ke cikin rikice-rikice da ya yi kamari a arewa maso yamma da kudu maso yamma, yankuna masu amfani da inglishi ko turanci, da arewa mai nisa inda kungiyar boko haram suke addabar al'umma, mutane sama da dubu 2 sun rasa rayukansu tun shekarar 2014 zuwa 2018 wasu da dama sun tsere daga gidajensu na samu mafaka a makwabciyar kasar Najeriya, sai kuma jahar gabas da ke da iyaka da babban birnin kasar jamhuriyar africa ta tsakiya Bangui inda yan bindigan seleka suke barazana a wannan pangaren kasar
A wannan bikin dai za a mayar da hankali ne kan zaman lafiya a kasar
Mako guda kafin wannan bikin, yan addinin krista sun bukaci zaman sulhu tsakanin yan aware da gwamnati, yau shekaru biyu kenan da kamaru ke fuskantar hare-haren yan aware inda mutane da dama suka rasa rayukansu tsakanin yan aware da sojoji kuma wasu mutane sama da dubu 15 sun tsere daga muhalinsu domin samun mafaka a kasar Najeriya wacce take da iyaka da kamaru.
Masha Allah