Wasu yan binduga wadanda ake zaton makiyaya ne sun kashe jami'in yansandan ciki na SSS da kuma soja guda, sannan wasu sun bace a wani harin da aka kai masu a jihar benue.
Jaridar Primiumtime ta Najeriya ta bayyana cewa akalla soja guda ne ya rasa ransa a wani harin da aka kai masu a karamar hukumar Logo na jihar a tsakiyar tarayyar Najeriya, sannan ake zatun maharan sun sace soja guda.
