
A yammacin jiya ne, aka bude taron kwalejojin Confucius na nahiyar Afrika na shekarar 2018 a birnin Maputo, hedkwatar kasar Mozambique. Shugabannin jami'o'in china da kasashen Afrika 41 da aka bude kwalejojin Confucius sama da 60, da wakilai kamfanonin china da hukumomi kimanin 300 ne suka halarci taron, abin da ya sa girman wannan taron ya kai sabon matsayin a karon farko a tarihi.
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar china Mista Li Zhanshu, bisa rakiyar shugaban majalisar dokokin kasar Mozambique, ya halarci bikin bude taron tare da yin jawabi.
A jawabinsa, shugaban jami'ar Eduardo Mondlane Orlando Antonio Quilambo ya bayyana cewa, kwalejin Confucius dake jami'arsa ta samu ci gaba sosai wajen koyar da chinanci da taimakawa ga mu'ammalar al'adu da sha'anin ba da ilmi tsakanin kasashen biyu tun kafuwarta a shekarar 2012.