Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce gwamnatinsa ta cimma nasarori masu yawa cikin shekaru uku fiye da abinda da jam’iyar PDP ta cimma a shekaru 16 da ta shafe tan mulki .
Buhari ya bayyana haka ranar Litinin a fadar sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Sanusi dake Dutse babban birnin jihar Jigawa, a cewar mai taimakawa shugaban kasar na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.
Ya ce faduwar darajar man fetur da ta fara a farkon shekarar 2016 bai hana gwamnatinsa daura damba na cimma wasu manufofin cigaba inda ta samu tarin nasara cikin shekaru uku fiye da shekaru 16 na jam’iyar PDP.
